Allah Gwani: Ko ka san me ke jujjuya ƙwayar idonka?


Kafin ka iya gane me ka gani ko ka hanga sai ƙwayar ido ta ɗauki hoton abin da ka gani sannan ta tura shi zuwa ƙwaƙwalwa domin ta fassara maka me ka gani.

Kuma ƙwayar ido ita kaɗai ba za ta iya jujjuyawa gefe zuwa gefe ko sama zuwa ƙasa da kanta ba domin ɗauko hoto sai da taimakon wasu tsokoki guda shida (6).

Waɗannan tsokoki shida sune ke riƙe da ƙwayar ido a cikin gurbin / kwarmin ido kuma sune ke jujjuya ƙwayar idon yayin da kake ƙoƙarin gani ko hangen wani abu.

Haka nan, waɗannan tsokoki na karɓar umarni ne daga jijiyar maganaɗisu ta 3, 4, da 6. Waɗannan jijiyoyin maganaɗisu sun samo asali ne yayin da ƙwaƙwalwa ta fitar da rassan jijiyoyi 12 da ke bai wa sassan kai umarni.

Matsaloli ga waɗannan tsokoki ko jijiyoyi zai haifar da matsalolin gani kamar: hararagarke, gani biyu-biyu, faɗowar murfin ido da sauransu.

Irin matsalolin da ke haddasa hakan sun haɗa da: rauni ga jijiyoyi ko tsokokin sakamakon bugu/haɗuran ababen hawa, danne/shaƙe ɗaya daga cikin jijiyoyin saboda bullin jijiyar jini a cikin ƙoƙon kai, ciwon siga, hawan jini, daji/kansar ƙwaƙwalwa, matsalolin da kan biyo bayan tiyatar ƙwaƙwalwa da dai sauransu.

Source: Physio Hausa 


KALLI YADDA SABON SARKIN ZAZZAU YA SHIGA FADA LATSA NAN


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN