Wasu yan Najeriya sun biya cikon kudin da Mojol Hospital ke bin Blessing Bassey, mata da ta haihu a Asibitin kuma ta kasa cika N95,000 da Asibitin ke binta daga cikin N250,000 da aka yi mata aikin fitar da Jariri wajen haihuw, a unguwar Choci da ke Shasha a birnin Lagos.
Bayan da Jaridar Punch ta ruwaito labarin ne a ranar 2 ga watan Oktoba 2020, mutane da dama a fadin Najeriya sun bukaci su biya mata kudin.
Daga cikinsu har da kungiyoyi kamar Right and Welfare of Traumatised Wives da Youths Initiative, Global Medical Organisation, da kuma sauran kungiyoyi da jama'a da basu son a ambaci sunansu.
Blessing yar shekara 27, ta gode wa Jaridar Punch da ta wallafa labarin, wanda ya yi sanadin da jama'a suka kawo mata dauki. Ta ce " Ba domin wannan Jarida ba, da har yanzu ina kwanciya a doron simintin wannan Asibiti a kasa tare da Jaririna".
Idan baku manta ba, Mojol Hospita ta rike Blessing ne ta hana ta komawa gida wata bakwai bayan ta haihu a Asibitin, bisa dalilin cewa ta kasa cika N95,000 ragowan kudin aikin tiyata N250,000.
KALLIYADDA SABO SARKIN ZAZZAU YA SHIGA FADA LATSA NAN
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/