Yan bindiga sun sace wani shugaban karamar hukuma


Yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace shugaban karamar hukumar Igannaa jihar Oyo.Comrade Jacob Olayiwola Adeleke.

Maharan sun sace Adeleke ne tare da Direbansa ranar Lahadi  25 ga watan Oktoba a kan hanyarsu ta bzuwa Okeho-Ado Awaye.

Shugaban yana kan hanyarsa ne ta zuwa Ibadan babban birnin jihar Oyo domin halartar taro tare da Gwamnan jihar kafin aukuwan lamarin.

Kakakin hukumar yansandan jihar Oyom Olugbenga Fadeyi ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce rundunar ta baza jami'an yansanda domin nemo tare da ceto shugaban karamar hukumar.

Kazalika yan banga na karamar hukumar sun baza nasu jami'an zuwa cikin gandun daji domin ceto shugaban karamar hukumar Mr. Adeleke


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN