Matar aure ta tsinke mazakutar mijinta bayan ya dirkawa wata budurwa cikil


Wata mata mai matsakaicin shekaru ta tsinke mazakutar mijinta a kan zarginsa da dirkawa wata budurwa ciki a yankin Appawa, wani bangare na karamar hukumar Lau na jihar Taraba. Kamar yadda jaridar Leadership ta wallafa, mijin mai suna Babangida wanda aka fi sani da Bangis yana cikin shekarunsa na 30.

Ya samu miyagun raunika a mazakutarsa bayan da matarsa ta yi yunkurin tsinka masa mazakutar a ranar Lahadi. Wata majiya daga yankin wacce ta sanar da The Nation, ta ce Bangis ya je kasuwa, bayan wahalar da ya sha sai ya isa gida inda ya kwanta bacci. "Da asubahi, matarsa ta tsinke masa mazakuta saboda dirkawa wata mata ciki da yayi.

Ya mayar da martani inda ya raunata ta da wukar da ya karbe a hannunta. “Makwabta sun ji ihunsu inda suka garzaya cikin gidan tare da tarar da wannan lamarin," majiyar tace. A lokacin da aka bukaci sanin dalilinta na kokarin tsinke masa mazakuta, matar ta yi martanin cewa ko a littafin bibul an bukaci a tsinke duk abinda zai sa a yi zunibi.

An mika Bangis asibiti kuma na gano cewa har a halin yanzu basu da da ko daya da matar. A wani labari na daban, Fusatattun matasa a karamar hukumar Yola ta jihar Adamawa sun garzaya ma'adanar tallafin rage radadin korona na jihar. Kamar yadda bidiyon ya bayyana, an ga matasan suna kokari har ta kai ga sun balle kofar ma'adanar inda suka dinga murna tare da ihu.

Source: LegitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN