An ci gaba da sace sace a Abuja, Lokoja da Calaba, lamari ya kazanta


Babban birnin jihar Kogi, Lokoja ya koma kamar filin daga a ranar Lahadi da daddare, bayan bata-garin da suka je sato kayan tallafin COVID-19 sun gamu da jami'an tsaro masu kulawa da kayan ADP da ma'adanar kamfanoni masu zaman kansu. Jami'an tsaron sun gamu da bata-garin da suka kwaso taki da shinkafa. Sakamakon gumurzun, mutane 4 ne suka rasa rayukansu, sai mutane 30 har da wani dan jarida da suka ji munanan raunuka.

Shigen lamarin da ya faru a Kogi, ya maimaita kansa a Calabar da Cross River, inda fiye da mutane 10 suka rasa rayukansu, ciki har da wata mata mai juna biyu, inda aka yi ta tafka gumurzu tsakanin bata-gari da jami'an tsaro tun ranar Asabar har Lahadi da daddare.

Bayan mutane 10 da suka rasa rayukansu a Calabar, jami'an tsaro sun samu nasarar damkar bata-gari a kalla 80. Sannan mata 2 sun rasa rayukansu sakamakon damben debo kayan tallafin COVID-19 a wata ma'adanar gwamnati da ke layin sakateriya a wuraren Gwagwalada da ke Abuja.Sun kwashi kayan abincin ma'adanar Bola Rotimi da sauran manyan 'yan kasuwa da ke jihar Kogi, inda suka kwashi shinkafa. Wasu daga cikin 'yan ta'addan sun balle ATM din wani banki da ke kusa da layin makabarta, wanda ke kallo wani wurin cin abinci.

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki iyaye da su koro yaransu da duk wasu kayan alatu da suka koma da shi gida, wanda sun san ba za su iya siya da kansu ba, The Cable ta wallafa.

Ya sanar da hakan ne bayan zanga-zangar EndSARS ta tsawon sati guda, wacce ta ja bata-gari suka yi ta wadaka da dukiyar gwamnati da ta al'umma a fadin kasa.

Source: LegitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN