• Labaran yau


  Yadda maigida ya sare kan matarsa da adda saboda ya kamata tana magana da makwabcinsa


  Wani magidanci mai tsananin kishi ya kashe matarsa kuma ya gundule kanta saboda ya ganta tana magana da makwabcinsa a kasar India.

  Rahotanni sun ce  Kinnar Yadav, mai shekara 40, ya dade yana zargin cewa matarshi mai suna Vimla, yar shekara 35 tana cin amanarshi.

  Makwabtansa da ke garin Baberu a Banda da ke jihar Uttar Pradesh ne suka rada wa Kinnar Yaday cewa matarsa Vimla tana lalata da makwabcinsa Rakivant Yaday a gidansa da ke makwabta da nasu.


   

  Bayanai sun nuna cewa ranar Juma'a 9 ga watan Oktoba, Kinnar ya dawo gida sai ya tarar da Vimla tana magana da Rakivant. Wanda bayanai suka ce yana tattaunawa da Vimla ne da take bashi shawara kan kalar Sa da yake son ya saya.

  Sai dai ganinsu tare suna magana ke da wuya, Kinnar ya matukar fusata, ya  dauko Adda ya raunata Rakivant, daga bisani ya kashe matarsa Vimla ya kuma sare kanta , sai ya dauki sararren kan ya kai caji ofis na yansanda.


   

  Yansanda na ci gaba da gudanar da bincike bayan sun kama Kinnar.

   


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda maigida ya sare kan matarsa da adda saboda ya kamata tana magana da makwabcinsa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama