An kashe wata mata a Badariya Birnin kebbi, har yanzu ba a gane yan uwanta ba


Bayan da aka kashe wata mata mai suna NJOKU ROSE NGOZI wacce aka fi sani da suna HELEN a mashayar B-JOY da ke kusa da Mammy Market, a unguwar Badariya da ke Birnin kebbi ranar 30 ga wata Satumba, har yanzu ba a gane yan uwanta ba.

Gwawar Helen yana dakin ajiye gawa a wani asibiti da ke cikin garin Birnin kebbi.

Rahotanni sun ce wasu mutane ne suka farmaki mashayar B-JOY da misalin karfe 4:30 na safe ranar 30 ga watan Satumba, suka ketare katangan ginin suka sami Helen, daga bisani suka kwace kudin ciniki da ta yi da dare.

Sai dai daga bisani an ga gawar Helen da safe, bayan an daba mata Almakashi a wuya kamar yadda Kakakin hukumar yansandan jihar Kebbi DSP Nafi'u Abubakar ya tabbatar.


 

Nafi'u ya kara da cewa an kama mutum biyar dangane da lamarin, kuma yansanda na ci gaba da bincike.

Bincike da muka gudanar, ya tabbatar cewa  NJOKU ROSE NGOZI, watau HELEN, yar asalin karamar hukumar Naze Owerri ce da ke karamar hukumar Owerri ta arewa a jihar Imo. Ta taba zama a garin Gwagwalada a birnin tarayya Abuja, da Kwannawa a Sokoto, da kuma garin Birnin kebbi.

Wata majiya ta bukaci duk wanda ya san yan uwanta ya taimaka ya bayar da bayani ta hanyar tuntubanmu.a kira ko SMS 08169229783.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN