Wani kamfani a Nijeriya ya kirkiro na’urar gano wayoyin Salular da aka sace


W
ani kamfani a Nijeriya mai suna -E.F. Network Ltd, ya kirkiro na’urar wayar sadarwa da ake amfani da ita wurin lalata wayar da barayi suka sace, domin hana barayi sakat da tseratar da muhimman bayanan dake cikin wayar daga hannun bata-gari a fadin kasar.
 
Mai magana da yawun kamfanin Mista Ameh Ochojila me ya bayyana haka a ranar talata a birnin tarayya Abuja.

Ochojila, Mai magana da yawun kamfanin ya ce, sun saka wa na’urar suna ‘ephonetaxi’ na’ura ce da zata taimaka wurin tseratar da dubban wayoyin sadarwa da barayi ke sace wa a fadin kasar dama duniya bakidaya.

“Na’urar ‘ephonetaxi’ Zata taimaka ka rufe dukkan wanda bashi da alaka da amfani da wayarka, ta yarda zaka mayar da wayar mara amfani tamkar ya rike fanko ,” kamar yadda ya bayyana.
Ya bayyana ce wa, na’urar an kirkiro ta ne don bawa wadanda suka mallaki wayoyin sadarwa kariya da kare bayanansu dake adane a cikin wayar daga sharrin barayi.

“Na’urar zata taimakawa masu wayoyi damar maido da bayanansu zuwa akwatun adana bayanai na E-mail dinsu.

“Sannan kuma zai bawa masu waya damar rufe rumbunan adanan hotunansu dake cikin wayar ta yadda ba yadda za a yi wani ya iya ganin hotunan wayar ko bidiyo ko sakonnin waya na masinja ko lambobin waya ida ba mai ita ba

“Na’urar na sanar da mai waya ya san an sauya masa katin sim dinsa na waya, sannan yana lalubu inda wayar take da daukar hutunan da barayin da suka sace wayar su kuma tura maka zuwa asusunka na Imel,” kamar yadda ya shaida.

Ochojila ya kara da ce wa: “Mai ainihin wayar yana da damar aiwatar da dukkan abunda aka lissafa don maganin barayi.“wani abun armashi ma shi ne, duk wanda ya siyi wayar to tamkar ya barnatar da kudinsa ne.”

Manajan mai kula da sashen kwararru na kamfanin ya yi karin haske ce wa, ana amfani da na’urar wurin gano masu garkuwa da mutane ta yadda na’urar zata bayyana hakikanin wuri da kuma lokacin da masu garkuwa suka sace mutum.

ya bayyana ce wa na’urar na daya daga cikin na’urorin da kamfanin ya samar don kaiwa matsayin da Nijeriya take fata na samu masu fasahar kirkire-kirkire a fannin kimiyya.

Egbuchulam ya ci gaba da ce wa, yanzu haka kamfanin ya bude ofishinsa a Abuja don kyankyasar kwararrun matasa masu kaifin basira a Nijeriya a bangaren kimiyya da sadarwa (IT). “Hakan zai baiwa Nijeriya damar samar da matasa da zasu zama masu jangora a fadin nahiyar Afirka.

“Kusan dukkan kamfanonin kimiyya a duniya suna sha’awar kasuwanci da Nijeriya saboda yanzu haka kamfaninmu zai dauki ma’aikata 1000 masu kaifin basira zuwa karshen shekara ta 2020,” kamar yadda ya shaida.

Kamfanin dillancin labarai a Nijeriya (NAN) ya bayar da rahoton da yake t

abbatar da ce wa a shekarar 2016 an sace sama da wayoyi 400,000 a Amurka, kuma galibin wayoyin an fitar da su kasashen duniya don a sake siyar da su.

Bincike ya tabbatar da ce wa, mafi galibin wayoyin da ake sace wa ana siyarwa ‘yan fashi da gungun masu aikata miyagun laifuka, ta yadda suke samun muhimman bayanan ta za su afkawa asusun Ajiya na banki su yi satar kudade ba tare da masu asusun sun Ankara ba. (NAN).)

Source: Jaridar Aminiya


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN