Buhari ya sake nada Farfesa Yakubu Mahmood shugaban INEC na tsawon shekara biyar


Shugaba Muhammadu Buhari ya sake nada shugaban hukumar INEC Farfesa Yakubu Mahmood a matsayin shugaban hukumar na tsawon shekara biyar na gaba.

Shugaba Buhari ya nada Mahmood a matsayin shugaban hukumar INEC a shekarar 2015, inda ya gaji tsohuwar shugaban hukumar Amina Zakari wacce ta shugabanci hukumar a matsayin Mukaddashin shugaba.

Hadimin shugaba Buhari Femi Adesina, ya tabbatar da labarin, ya kuma ce shugaba Buhari ya aika sunan Mahmood zuwa Majalisar Tarayya domin amincewa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN