Mun ba talakawa tallafin Naira biliyan 6 a jihar Zamfara - Minista Sadiya Farouk


Ministan jinkai da bayar da agajin gaggawa Sadiya Umar-Farouq ta ce ma'aikatarta ta bayar da taimakon Naira biliyan N6b ga talakawa a kananan hukumomi 14 na jihar Zamfara. Ta yi wannan jawabi ne ranar Talata 27 ga watan Oktoba a jihar Zamfara.

Ta ce an tura wa talakawan kudaden ne karkashin shiri na musamman na tura kudi da ake kira 2020 Conditional Cash Transfer (CCT).

Ta ce talakawa 130,000 ne suka amfana da shirin daga kananan hukumomin Anka, Bungudu, Birnin Magaji, Kaura Namoda, Tsafe, da Talata Mafara.

Ta ce wadanda suka amfana sun sami daga N30,000 zuwa N80,000 wanda ya danganta da lokacin da suka cika takardun neman taimakon.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN