Sana'a madogara ga mace, taimaka wa miji da samun nassarar rayuwa - Saratu dan Sokoto

Saratu Dan Sokoto

Sunana malama Saratu dan Sokoto kuma na fara sana'a sama da shekara biyu. Na taba yin aure kuma ina da yara biyu.Na sa yarana makarantar boko da na Arabiyya, kuma ina kula da yara na da sana'ar da nike yi na sayar da abinci a Taushi Plaza da ke kan Titin Ahmadu Bello a garin Birnin kebbi.

NASSARORI

Na sami nassarori da yawa a wannan sana'a. Na godo wa Allah da ya taimaka mini ya karbi kuka na. Na dogara ga kaina da diyana da duk wanda ya rabe ni.Ina kasuwanci na kuma Alhamdu lillahi.

MATSALAR RASHIN SANA'A GA MACE

Akwai babban matsala ga zaman diya mace matukar bata da sana'ar yi, ya kamata mace ta sami yanayi na dogara da kanta saboda halin rayuwa, akwai yau akwai gobe. Misali, mahaifi na Allah ya yi masa rasuwa fiye da shekara 7 da suka gabata.

Ko a lokacin da nike gidan mijina ina sayar da ababe kanana da mace ke iya sayarwa a cikin gidanta. Ban taba zama bana sana'a ba. Da Allah ya kaddari na dawo gida sai na dogara ga kaina, kuma na zauna na duba na tsawon lokaci abin da ya kamata inyi.

Zaman gida babu sana'a babu dadi ga diya mace, domin ko da a gidanku ne idan baki da komi, ba wani abin da za a yi da ke. Ba komi kike so za a yi maki a gida ba, kuma ko da za a yi maki shi, wani sa'ilin za a iya ja maki rai kafin a yi. Idan kina da abin ki za ki iya dauka ki biya ma kanki bukata.


SANA'AR DIYA MACE DA TAIMAKA WA MIJI

Ko da kina gidanki, duk irin arziki da Allah ya yi wa maigidanki, shi kanshi yana son ki taimaka mashi da wani abu. Idan baki da sana'a babu yadda za ayi ki taimaka wa kanki, kullum bani, bani, yakan haifar da yawan matsaloli a gida.

SHAWARA DA MAFITA GA MATA

Shawaran da zan ba yan uwana mata shi ne ya kamata mu aje girman kai, mu aje tunanin komi mu duba abin da gobe za ta yi, bai kamata a ce iyaka ta in wanke in goge ba, yau ina wajen aure, ko wajen lalura wannan ya kira ka wancan ya kira ka. 

Muddin kina da sana'a, idan kin tashi da safe za ki fuskanci aikin sana'arki ne, har ki hada kudi ki fitar da abin da kika kashe bisa lissafi kuma ki fitar da riba. Saboda haka yawace yawace ba alhairi bane, illa a fuskanci sana'a har kafin Allah ya sauka wa mace da ijabar aure.

Kuma idan aka yi aure, akwai sana'oi da yawa da matan aure zasu iya yin su a cikin gida kuma ki sami kudi. Shawara da nike kara ba yan uwanmu mata shine a fuskanci sana'a mu sami na kan mu domin yanzu an bar zaman banza.

BURI DA HAKURI

Buri na ya cika na sa yara na a makaranta, Allah ya cika min burina kuma yana kan cikawa, domin duk abin da ka yi niyya na alhairi Allah zai cika maka shi. Buri na na biyu shi ne in ga Allah ya nuna min na yi aure. Saboda zaman titi bai da dadi. Idan babu hakuri, kasuwanci bai zuwa ko ina.

Amma idan ka yi hakuri, za ka cimma hakurinka, saboda kafin in saba da kasuwanci na wahala. Na wahala domin wani zai iya zuwa ya yi maka maganar banza kan abin da bai kai ya kawo ba, wani lokaci akan sami wadanda ke zagina.

Saboda haka idan baka jure ba, kasuwancin ba zai je ko ina ba, saboda haka sai na jure, kuma Allah ya bani alhairi har wanda ba a tunani ko zaton cewa za a samu a cikin wannan kasuwanci na sayar da abinci. Allah ya nuna min na bar titi lafiya, ya nuna min na yi aure, kuma auren idan na yi ya tabbata har illa ma sha Allahu.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN