EndSars: An kashe mutum 2, an kone ofishin yansanda, an rufe makarantu a jihar Oyo


An kashe mutum biyu a unguwar Ojoo da ke birnin Ibadan babban birnin jihar Oyo ranar Talata 20 ga watan Oktoba bayan masu zanga zangan EndSars sun banka wuta a ofishin yansanda da ke Ojoo.

Wani ganau ya gaya wa Jaridar Daily Trust cewa matsalar ta samo asali ne bayan masu zanga zanga sun dakile hanyar shiga ofishin yansanda. Lokacin da yansanda suka yi kokarin jaye shinge da masu zanga zanga suka sa, sai suka nuna turjiya.

Sakamakon haka aka sami tashin hankali da ya yi sanadin mutuwar mutum biyu.

Wakilin Daily Trust ya labarta cewa an kulle yawancin ofisoshin yansanda da ke birnin Ibadan bayan aukuwan lamarin.

Ofisoshin yansanda na Apata da rundunar shiya ta Iyaganku an rufe, kazalika ofishin yansanda na Omi-adio , Mokolda Agodi duk an rufe su.

Gwamna jihar Oyo Engr. Seyi Makinde, ya umarci rundunonin tsaro na jihar su fuskanci matsalar a wani tsari da salon fuskantar kalubalen tsaro da aka rada wa suna " Operation Burst" saboda a dowo da doka da oda a birnin Ibadan.

Kazalika Gwamnan ya bayar da umarnin rufe makarantu har zuwa karshen mako saboda dalibai su sami kulawa wajen iyayensu..


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN