Rundunar Soji ta karbe iko da tsaron gidan gwamnatin jihar Imo


Da sanyin safiyar ranar Laraba ne sojoji suka isa 'Douglas House' bayan dokar ta bacin da gwama ya saka ta fara aiki, Daily Trust ta wallafa. Dandazon masu zanga-zanga sun yi tururuwar fitowa domin cigaba da gudanar da zanga-zanga duk da sanarwa da gwamnan jihar, Hope Uzodinma, ya fitar da yammacin ranar Talata.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa gwamna Uzodinma ya fitar da sanarwar a kurarren lokaci. Yawanci mazauna jihar, da suka hada da daliban da ke zuwa makaranta, basu san an saka dokar ta baci ta 24 ba. Duk da babu labarin samun wata barna yayin zanga-zangar ENDSARS a jihar Imo, wasu matasa sun yi yunkurin kona wani ofishin 'yan sanda a Ihiagwa.

Da yawan mazauna jihar sun gaggauta komawa gidajensu da yammacin ranar Talata bayan sanar da baza 'yan sandan kwanton da tarzoma a fadin Najeriya. A wani labari na daban, Bata-garin matasa a ranar Laraba sun banka wa gidan iyayen gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, wuta.

Gidan yana kan titin Omididun inda suka dinga jifansu da duwatsu. Gwamna Sanwo-Olu ya saka dokar ta baci ta sa'o'i 24 a jihar sakamakon zanga-zangar EndSARS a ranar Talata. Daga bisani sojoji sun shiga lamarin, abinda ya kawo mutuwar a kalla mutane 7 wadanda da yawansu matasa ne. Bayan wani lokaci, matasan sun yi nasarar kone gidan kurmus.

Source: Legit

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN