Kisan Lekki: Sarkin Musulmi ya umurci Musulmai su yiwa Najeriya addu'a na musamman ranar Juma'a


Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta shari'ar Musulunci a Najeriya (NSCIA), Alh Muhammad Sa'ad Abubakar, ya alanta ranar Juma'a matsayin ranar addu'a ta musamman ga Najeriya.

Sarkin ya ce umurci Musulman Najeriya su yi addu'a bisa rikicin da yayi sanadiyar asarar rayuka da dukiya a Legas, Benin da wasu jihohi. Mai Alfarma ya jaddada cewa addu'a da komawa ga Allah kadai ya rage a yiwa kasar nan domin samun zaman lafiya.

Sarkin Musulmi a jawabin da ya saki a Abuja ranar Laraba, ya bukaci dukkan Limamai su yi Khuduba kan rikicin dake faruwa a kasar domin kwantar da hankalin mabiya Jawabin da Femi Abbas, shugaban kwamitin yada labarai na NSCIA ya rattafa hannu, an bukaci dukkan Musulman Najeriya su hada kai da Limamansu wajen addu'a Allah ya zaunar da kasar nan lafiya.


Yace, duk wanda yayi imani da Allah, babu matsalar da ba zata iya magantuwa da addu'a ba. Hakazalika Sarkin Musulmi ya bukaci Musulmai yan Najeriya dake kasashen wajen su sa baki wajen addu'a. Daga cikin abubuwan bayan-bayan da ya faru a yau. wasu mutane da ake zargin 'yan ta'adda ne sun balle babbar kotun Igbosere ta jihar Legas, inda suka yi awon gaba da wasu takardun kotun.

A Bidiyon da The Cable suka wallafa, an ga wadanda ake zargin 'yan ta'addan ne suna fita daga kotun da wasu kayan amfanin kotun

Source: LegitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN