• Labaran yau


  Mutum 3 sun tone kabari 10 suka datse kawunan mamata domin tsafi


  Yansanda sun gurfanar da wasu uku a gaban Kotun Maajistare a Ado-Ekiti bisa zargin hakar Kabari suka tone gawakin 10 da aka binne kuma suka yanke kawunasu bisa dalilan tsafi.

  Wadanda aka kama su ne Kola Fatoye mai shekara 40, da Abimbola Fatoyedan shekara 35, da Ahmed Ojo, shekara 56 a Duniya.

  Mai gabatar da kara ta yansanda Monica Ikebuilo ta gaya wa Kotu cewa wadanda ake zargi sun aikata laifin ne tun watan Maris zuwa Satumba a garin Prun-Ekiti.

  Ikebuilo ta ce gawakin da mutanen suka tone na Philip Akintayo, Moreani Ajayi da wasu mutun takwas ne., kuma sun yi hakan ne bisa dalilan tsafi, kamar yadda ta gaya wa Kotu.  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mutum 3 sun tone kabari 10 suka datse kawunan mamata domin tsafi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama