Babban magana: An kama Lauyan bogi a cikin Kotu yana tsakar kare mai laifi


Yansanda ajihar Ogun sun kama wani Lauyan bogi, dan shekara 47 mai suna  Tajudeen Olufemi Idris ranar Juma'a, yayin da ya gabatar da kansa a matsayin Lauya a cikin Kotu domin kare wani mutum.

Kakakin hukumar yansandan jihar Ogun Abimbola Oyeyemi ta ce an kama Lauyan bogin ne a cikin Kotun Majistare na 6 da ke Ifo, lokacin da ya gabatar da kansa ga Cif Majistare I.A Arogundade a wata shari'a tsakanin wasu mutane biyu Ifeanyi Chuckwu da Ayo Itori.

A cikin Kotun, Lauyan bogin ya ce ya zo ne ya wakilci daya daga cikin wanda ke da shari'a a gaban Kotun kuma ya zo ne daga ofishin Lauya mai suna Tajudeen O. Idris & Co Chamber.

Sai dai Kakakin ta ce, yanayinsa da yadda ya gabatar da kansa ga Kotu, ya haddasa shakku kan hakikanin gaskiyar lamarinsa. Ta ce sakamakon haka, Mai shari'a ya tambaye shi ko a wane shekara ne aka kira shi zuwa Bar na Lauyoyi. Ta ce wanda ake zargin ya ce a 2009 ne aka kira shi zuwa Bar.

Sai dai bincike da aka gudanar na jerin sunayen Lauyoyi da aka kira zuwa Bar a shekarar 2009 babu sunansa a ciki. Sakamakon haka yansanda suka yi awon gaba da shi.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN