Malamin Jami'ar jihar Kebbi mai shekara 38 ya rasu a barin wutan yan bindiga a Abuja


Wasu yan bindiga dadi sun kashe wani malamin  Jami'an jihar Kebbi mai suna Abdullahi Abubakar Dakingari dan shekara 38 a Duniya kafin ajalinsa.

Rahotanni sun nuna cewa Abdullahi ya je birnin Abuja ne domin duba mahaifinsa da aka kwantar a wani Asibiti sakamakon rashin lafiya.

Kawun marigayin mai suna Abubakar Mu'azu Dakingari, ya tabbatar wa jaridar Daily Trust cewa lamarin ya faru ne ranar Laraba 14 ga watan Oktoba , bayan an harbe shi da bindiga a unguwar Life Camp da karfe 10:30 na dare bayan ya sami kanshi a tsakiyar harbe harbe da bindigogi daga wasu mutane.

An binne shi bisa tsarin addinin Musulunci. Ya rasu ya bar mata daya da yaro daya.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN