Hukuncin zanga-zanga a Shariah - Dr. Ahmad Mahmud Gumi


Tsokacin Edita: Dukkan abubuwan da zasu karanta a wannan rubutu ra'ayin marubucin ne ba ra'ayi Legit.ng Hausa ba. 

Haka zalika Mujallar ISYAKU.COM ta bi sahun bayanin Edita na Legit.ng

Hukuncin zanga-zanga a Shariah Daga Dr Ahmad Gumi 

"Idan zanga-zanga ce da nufin ibada ce ita kanta watau 'ta-abbudiyah' to, bidi'ah ce domin babu Zanga-zanga cikin ibadun musulunci. 

Kamar tattaken arbaeen na Shiah, ko maulidai ga masu yin haka. Idan kuma ita babin mu'amalah ce da siyasah, to dole ayi tafsili.

In tanada amfani a mahangar shariah to hukuncin ta yakan fada akan hukunce hukuncen shariah na wajibci, ko mustahabbi ko Halas ko makaruhi ko Haram. 

Zanga-zangar da zata kawo sawyin mulki ko bijirema shugabanni Musulmi masu adalci ko marsa adalci, jairai, masu mugunta, haramun ce. (a saurari Karin bayani daga baya) Zanga-zangar da zata kawo sawyin halin jamaah zuwa inganta rawuwarsu mustahabbi ce.

Zanga-zangar da zata kawo sawyin halin jamaah zuwa inganta addinin su yajibace amma da sharadin rashin haifar da musiba wadda tafi yadda ake kafin ayita. 

Zanga-zangar da zata kawo rarrabuwar kan jamaah ko salwantar dukiya ko rayuka haramun ce magana guda. To me Saya aka haramta Zanga-zangar juye mulki daga hannun Musulmi ko da jairine?

1. Mulki na Allah ne - Subhanahu Wa Taala, Shi Ya haramta Musulmi suyi jayayya kan mulkinSa.

2. Duk abunda da zai kai ga fada tsakanin Musulmai haramunne.

3. Tashin hankali domin neman mulki Bai haifar da da Mai ido. Duk locakin da mutane suka hada kansu domin su juye mulki sai suma sun hainci kanuwansu. 

Karshenta a wahala fiye da farko. Saboda haka, a irin wannan tsari, na demokiradiya, dama yazo cikin kundinshi da halarcin Zanga-zanga ta lumana saboda haka baa iya haramta ta da sunan addini.

Sai Dai, idan akwai yuyuwar shigan muyagun mutane da zasu karkatar da ita zuwa wata muguwar manufa ta cutar da addini ko yanayi ko salwantar da dukiya ko rayuka ko cin mutuncin mutane to wannan haramun ne a Shariah. Wallahu 'Alam.

Allah Ya bamu dacewa, Ya kawo muna taimako daga wurinsa da kuma Zaman lafiya. Kuma Ya hada kanmu akan gaskiya da dukkan alheri. Amin."

Source; Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN