Mahaifi ya sare hannun dansa bisa zargin ya sace masa N150,000


Wani magidanci mai suna Gregory Enweaso dan shekara 48 a jihar Anambra da ke kudu maso arewacin Najeriya, ya sare hannun dansa mai shekara 33 mai suna Abuchi, saboda bai gan kudinsa ba kuma yana zargin cewa yaron ne ya sace kudin.

Sai dai yaron ya yi zargin cewa ba haka zancen yake ba. Ya ce mahaifinsa ya hada baki da wasu yan uwansa domin su kashe shi saboda dalilan tsafi.

Ya kara da cewa tun farko, mahaifinsa tare da wani dan uwansa, sun kai karar shi wajen yansanda cewa ya yi masu sata. Kuma aka tsare shi a ofishin yan sanda. Amma daga bisani aka bayar da shi Beli, kafin suka sake kitsa wannan lamari.

Kakakin hukumar yansandan Jihar Anambra  SP Haruna Mohammed, ya tabbatar da faruwar lamarin,. Ya ce mahaifin yaron ya shigar da kara cewa dansa Abuchi ya sace N150,000 daga kudin da suka samu bayan wani biki da aka yi a gidan. Ya ce an kai Abuchi Asibiti domin samun kulawan Likita yayin da ake ci gaba da bincike.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN