Daduminsa: Batagari sun kai hari ofishin gwamna Akeredolu, hotuna da bidiyo


Rahoton da Legit.ng ke samu daga jaridar Vanguard ya tabbatar da cewa wasu batagari sun kai hari babban ofishin gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, da ke Akure.

A hotuna da faifan bidiyo da Vanguard ta yada, an ga matasa na kone-kone yayin da suke lalata ofishin da Akeredolu ya yi amfani da shi yayin yakin neman zabensa da aka kammala ranar 10 ga watan da muke ciki.

Da sanyin safiyar ranar Laraba ne sojoji suka isa 'Douglas House' bayan dokar ta bacin da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya saka ta fara aiki, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Dakarun rundunar soji sun mamaye hanyoyin shiga gidan gwamnatin jihar Imo, 'Douglas House'.

Sojojin sun yi hakane domin hana fusatattun ma su zanga-zanga samun damar shiga gidan.

Dandazon masu zanga-zanga sun yi tururuwar fitowa domin cigaba da gudanar da zanga-zanga duk da sanarwa da gwamna Uzodinma ya fitar da yammacin ranar Talata.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa gwamna Uzodinma ya fitar da sanarwar a kurarren lokaci.

Yawanci mazauna jihar, da suka hada da daliban da ke zuwa makaranta, basu san an saka dokar ta baci ta 24 ba.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN