Imam Muhktar ga shugaban Faransa: Allah zai haska addinin Musulunci ko da Kafirai basa so


Limamin babban Masallacin Juma'a na jihar Kebbi (Central Mosque) Imam Muktar Abdullahi (Walin Gwandu), ya caccaki shugan Fransa da mukarrabansa bisa manufarsu ta cutar da Manzon Allah, addinin Musulunci da Musulmi. Imam Muhktar ya yi wannan jawabi ne a Hudubarsa kafin Sallar Juma'a.

KADAN DAGA ABIN DA HUDUBAR TA KUNSA

Abin da shugaban Faransa Emmanuel Macron da mukarrabansa ke son su yi a yau suna son su mayar da Manzon Allah abin wasa, su wulakanta shi , su zage shi, manufarsu su dushe hasken addinin Musulunci. Allah kuma ya ce shi mai cika hasken addininsa ne ko Kafirai basa so.

Yanzu haka Faransa na kokarin ta kirkiro wani Musulunci sabo domin su batar da al'umma, sun yi masa suna Musuluncin Faransa. Haka suka yi suka gurbata littafansu.tun farko kuma Allah ya bamu labarinsu.

Suna zaburar da kiyayya da tashin hankali, suna zaburar da fitinu, tare da zaburar da kiyayya tsakanin mutane da kasashe. yanzu shi ne namiji mai zaruntaka,

Shugaba  Recep Tayyip Erdo─čan, shugaba kasar Turkey, Gwarzo mai kishin addininsa, mai kishin al'ummansa. Ya yi abin da ya kamata, a lokacin da ya kamata, amma wasu suna ganin cewa Erdogan bai da yancin mayar da martani ga shugaban Faransa.

Allah shi albarkaci Erdogan, shi  yawaita mana shugaba irin Tayyip Erdogan, shi yawaita mana irinsu. saboda kokarinshi na taimaka wa Musulunci da Musulmi. Kuma shi tabad da shugaban Faransa da wadanda suka bi sawunsa. da kiyayya ga Musulmi da Musulunci.

LATSA KASA KA KALLI CIKAKKEN BIDIYON HUDUBANLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN