Sojojin Najeriya za su yaƙi masu yaɗa farfaganda a kafofin sada zumunta


Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana aniyarta ta ƙaddamar da Atisayen Murmushin Kada karo na shida, wanda a turance aka fi sani da Crocodile Smile.

Sai dai a wannan karon, atisayen zai mayar da hankali ne wurin bin diddiƙi da kuma gano masu watsa farfagandar ƙarya a shafukan sada zumunta.

A wata sanarwa da mai magana da yawun sojojin ƙasar Kanal Sagir Musa ya fitar, ya bayyana cewa wannan ne atisaye na farko makamancin haka da za a gudanar a tarihin sojoji a Afrika.

Ya kuma bayyana cewa wannan atisayen na murmushin kada zai sa ido ga 'yan Boko Haram da ke guduwa daga arewa maso gabashin ƙasar zuwa sauran sassan Najeriya domin gano su.

Za a ƙaddamar da atisayen ne a ranar 20 ga watan Oktoba zuwa 31 ga watan Disambar 2020.

Source: BBC


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN