Wani malamin Jami'an Mkar Moses Tarnongo, matarshi tare da yayansu uku sun mutu a hadarin mota a jihar Benue.
Haka zalika wasu mutum biyu tare da wani malamin Jami'an Mkar mai suna Joshua Leva, ya mutu a cikin hadarin da ya auku ranar Asabar 10 ga watan Oktoba a garin Gbatse da ke kan hanyar Ugbema Adikpo a karamar hukumar Ushongo a jihar Benue.
Magatakardar Jami'an Mkar, Rev. Emmanuel Astor, ya tabbatar da faruwar lamarin a Makurdi, ya ce Moses Tarnong ya mutu a hadarin tare da matarsa da yaransa guda uku. haka zalika wasu malaman guda biyu na sashen karatun aikin Jarida sun mutu.
Ya ce wadanda suka mutu suna kan hanyarsu ce ta zuwa garin Adiko da ke karamar hukumar Kwande domin zantawa da wani shehin malamin addini kafin faruwar hadarin.
Wani ganau ya ce lamarin ya faru ne bayan direban Tilera ya yi kokarin kauce wa shingen binciken yansanda domin yana dauke da sabuwar mota a Tileran, garin haka ne ya je ya ci karo da motar malamin Jami'an, kuma ya murkushe su nan take.
Ganau ya kara da cewa an dauki awanni da dama kafin a iya ciro mamatan daga motar kirar Toyota mai lamba MKD-300-NH.
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/