Hotuna: Yadda babban mota ta murkushe mahaifi, mahaifiya, 'ya'yansu 3 da wasu mutum 2

Wani malamin Jami'an Mkar Moses Tarnongo, matarshi tare da yayansu uku sun mutu a hadarin mota a jihar Benue.

Haka zalika wasu mutum biyu tare da wani malamin Jami'an Mkar mai suna  Joshua Leva, ya mutu a cikin hadarin da ya auku ranar Asabar 10 ga watan Oktoba a garin Gbatse da ke kan hanyar Ugbema Adikpo a karamar hukumar Ushongo a jihar Benue.


Magatakardar Jami'an Mkar, Rev. Emmanuel Astor, ya tabbatar da faruwar lamarin a Makurdi, ya ce  Moses Tarnong ya mutu a hadarin tare da matarsa da yaransa guda uku. haka zalika wasu malaman guda biyu na sashen karatun aikin Jarida sun mutu.

Ya ce wadanda suka mutu suna kan hanyarsu ce ta zuwa garin Adiko da ke karamar hukumar Kwande domin zantawa da wani shehin malamin addini kafin faruwar hadarin. Wani ganau ya ce lamarin ya faru ne bayan direban Tilera ya yi kokarin kauce wa shingen binciken yansanda domin yana dauke da sabuwar mota a Tileran, garin haka ne ya je ya ci karo da motar malamin Jami'an, kuma ya murkushe su nan take.


 

Ganau ya kara da cewa an dauki awanni da dama kafin a iya ciro mamatan daga motar kirar Toyota mai lamba MKD-300-NH.


DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN