Tsohon dan takaran shugaban kasa Adamu Garba, ya maka shugaban Twitter Jack Dorsey a Kotu saboda nuna goyon baya ga masu zanga zangan EndSars a Najeriya.
Adamu ya maka Dorsey a Kotu yana neman Dorsey ya biya Gwamnatin tarayyar Najeriya Dalan Amurka Biliyan daya kwatankwacin Naira Biliyan N380.
Wani faifen bidiyo da ya bayyana a yanar gizo ya nuna Adamu yana jaddada kalamansa a kan Dorsey cewa sa hannunsa a matsalar Najeriya ya kara haifar da rudani da tashin hankali a cikin kasa.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari