Saurayi ya yi wuff da wata budurwa bayan budurwarsa na dauke da cikinsa wata 7


Wata mata 'yar Uganda ta shiga cikin mummunan tashin hankali bayan sanin cewa saurayin da take da cikinsa ya aura wata.

Wata mata mai da daya ta sanar da Mywedding.co.ug cewa sun fara soyayya da wani mutum mai suna Norman a 2008, ranar da suka fara haduwa sai soyayyar juna ta ratsa zuciyoyinsu.

Matar tace a ranta tayi yakinin cewa soyayyar su wata rana zata kai ga aure.

A lokacin da ta gano tana da ciki da Norman, tayi farin ciki matuka, saboda zata hada zuri'a dashi.

Masoyin nata, Norman, yana aikin gwamnati kuma yana tafiye-tafiye zuwa garuruwa daban-daban, don haka basu samun damar ganin juna sosai, sai dai su na yawan magana ta waya.

Hankalinta ya yi matukar tashi bayan ta fahimci cewa yana tarayya da wata mata. Tace bayan ta sanar da Norman tanada juna biyu ya amince ta haife jaririn.

Saurayi ya yi wuff da wata budurwa bayan budurwarsa na dauke da cikinsa wata 7. Hoto daga Mywedding.co.ug

Tace ta fara zargin wani abu a lokacin da aminiyarta ke tambayarta idan ya yarda ta haife jaririn, ashe tana da ciki wata 7 yayi aurensa. Bata yarda da hakan ba sai bayan taga hotunan bikin.

A wani labari na daban, an dakatar da dalibai 20 'yan aji 4 da ke babbar makarantar sakandire ta Loreto a Zimbabwe sakamakon kamasu da laifin lalata da juna a watan Yuli.

Da yake makarantar ta maza da mata ce, an kama daliban tsirara suna lalata a inda yara matan ke kwana na makarantar da ke Silobela, yayin da suke shirin fara jarabawar watan Yuni zuwa Yuli.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN