Yanzu-yanzu: Buhari ya nada Sanusi Garba sabon shugaban hukumar kula da wutan lantarki a Najeriya


Shugaba Muhammadu Buhari ya zabi wadanda yake son a nada sabbin shugabannin hukumar lura da wutar lantarki a Najeriya watau NERC.

Shugaban kasar ya aike da sunayensu majalisar dokokin tarayya domin tabbatar da su.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Ibrahim Lawan, ya karanta wasikar da Buhari ya aiko musu a zauren majalisa ranar Talata, 20 ga watan Oktoba, 2020.

Wadanda Buhari ya zaba sune:

1 . Engr. Sanusi Garba - Shugaba

2. Musiliu Olalekan Oseni - Mataimakin shugaba

3. Aisha Mahmud - Kwamishana


Yanzu-yanzu: Buhari ya nada Sanusi Garba sabon shugaban hukumar kula da wutan lantarki a Najeriya Hoto: @mobilepunch

A bangare guda, majalisar dattawa, a ranar Talata ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa 'yan Najeriya jawabi nan take a kan zanga-zangar da matasa ke yi a jihohin kasar game da cin zali da 'yan sanda ke yi da kuma neman kawo gyara a gwamnati.

Majalisar ta kuma bukaci jami'an 'yan sanda su bawa matasa da ke zanga-zangar ta EndSARS kariya daga 'yan daba da ke neman mamaye zanga-zangar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN