Dazunnan: An kashe mutum uku aka kone su bisa zargin yunkurin sace wani mutun


An kashe kuma aka kone wasu mutane uku a garin Akpabuyo, na jihar Cross River bayan yunkurinsu na sace wani mutum ya ci tura da tsakar ranar Asabar 17 ga watan Oktoba.

Daiky Trust ta ce wani ganau ya ce mutanen sun yi kokarin sace wani mutum ne da tsakar rana, amma sai ya yi ta ihun neman taimako wanda hakan ya ja hankalin jama'a kuma suka afka masu da duka da karafa, katako da sauran makamai kuma daga bisani aka banka masu wuta.

Wata majiya ta yi zargin cewa akan kai wadanda aka sace ne a karamar hukumar Akpabuyo.

Sace mutane ya yawaita a fadin jihar cikin shekaru uku da suka gabata

Sai dai nan take Kwamishinan yansandan jihar ta hannun Kakakin yansandan jihar ya fitar da sanarwar  Allah wadai da matakin kashe mutanen nan take ba tare da bincike ba, kuma ya bukacio jama'a su daina daukan doka a hannunsu ta hanyar yin hukuncin kato.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari