Da ɗumi-ɗumi: An saka dokar hana fita a fadin jihar Kaduna


Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya saka dokar hana fita a dukkan ƙananan hukumomin da ke jihar Kaduna.

Tunda farko, gwamnan ya sanar da saka dokar hana fitar ne a kananan hukumomi biyu wata Kaduna ta Kudu da kuma Chikun.

Amma daga bisani ya kara fadada dokar zuwa dukkan kanananan hukumomin jihar inda ya ce an yi hakan ne don kiyayye lafiyar al'umma da dukiyoyinsu.

Gwamnan ya fitar da sanarwar ne a shafinsa na Twitter a ranar Asabar 24 ga watan Oktoban 2020.

Legit.ng ta ruwaito cewa gwamnan ya saka dokar ne bayan kutse da wasu mutane suka yi a ma'ajiyar abinci da ake zargi na korona ne a ƙananan hukumomin biyu.

Sanarwar mai dauke da sa hannun kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ta ce an bawa jami'an tsaro umurnin kama duk wanda aka samu ya saba dokar hana fitan.

"An umurci jami'an tsaro su kama duk wanda aka samu yana fashi ko lalata kayayyaki a kuma gurfanar da shi gaban kotu," a cewar sanarwar.

Ya kuma yi kira da mazauna jihar su rungumi zaman lafiya su guji duk wani abu da ka iya tada hankali ko rushewar doka da oda.

A wani labarin, wasu da ake zargi ƴan daba ne a ranar Asabar sun kai hari gidan Sanata Teslim Folarin dan jamiyyar APC mai wakiltar Oyo Central da ke Ibadan sun sace kayan tallafi da kuɗin su ya kai N200m.

Folarin ya tabbatar da faruwar mummunan lamarin yayin wani shirin gidan rediyo a ranar Asabar a Ibadan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN