Wata sabuwa: Miyetti Allah ta bankaɗo wanda ke ɗaukar nauyin Zanga-zanga


Kungiyar Fulani makiyaya a Najeriya, Miyetti Allah, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yiwa zanga-zangar EndSARS da ke gudana rikon kazar kuku, cewa gangamin wani shiri ne na durkusar da gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Da yake magana a wata hira da jaridar The Sun, Shugaban kungiyar, Bello Abdullahi Bodejo, ya ce duk da an gaskata manufar zanga-zangar, ta zarta lokacinta.

Shugaban Miyetti Allah, wanda ya bayyana cewa ya yi farinci lokacin da zanga-zangar ta fara, ya tabbatar da cewa mambobin kungiyar da dama sun dandana kudarsu a hannun rundunar SARS da aka rushe.

Bodejo ya bayyana cewa kamata yayi a ce masu zanga-zangar sun dakatar da gangaminsu sannan su bar tituna tunda gwamnati ta amsa bukatunsu.

Ya ci gaba da bayyana cewa rashin komawar masu zanga-zanga gidajensu ya nuna cewa “akwai wani boyayyen ajanda a zanga-zangar.” A cewar Shugaban kungiyar Miyetti Allah, “wani dan siyasa a kudu maso yamma ne ke daukar nauyin zanga-zangar.” 


Da yake ci gaba da magana, Bodejo ya bayyana cewa ana kama Fulani makiyaya a kan dalilai marasa tushe yayinda jami’an SARS ke neman a biya kudi tsakanin "N500, 000 da N600, 000 na beli kafin su saki mutum; sun matsawa mutanenmu.”

“Akwai wani boyayyen ajanda a zanga-zangar. Ga dukkan alamu, ba wai yan siyasa bane kawai, illa wani dan siyasa da ya matsu daga yankin kudu maso yamma ne ke daukar nauyin wannan gangami. 

Wannan ne dalilin da yasa muka ki yin shiru, sannan muka yanke shawarar sanar da kasar abunda ke faruwa saboda mafi akasarin mutane basu san ma’anar abunda ke faruwa ba.

“Ba zanga-zanga bane kuma; wani dan siyasa da ya matsu wanda ke ganin cewa ba zai kai labari ba a 2023 shine ke kada gangar nan ga matasanmu.”Tsohon shugaban kasar ya kasance daya daga cikin shugabannin Najeriya da ke raye wadanda Buhari ya gayyata zuwa wani taro na yanar gizo a ranar Juma’a.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN