Tsinkewar Laka da abubuwan da ya kamata ka sani


Ƙwaƙwalwa ce cibiyar sarrafa saƙo da fassara shi. A yayin da saƙo ya sauko daga ƙwaƙwalwa zai bi ta laka, wato "spinal cord" a turance, daga nan, laka za ta tura saƙon zuwa sashin da aka nufa da shi ta hanyar manya da ƙananun jijiyoyin laka, wato 'spinal nerves' a turance.

Tsinkewar laka kuwa na nufin tsinkewar sadarwa tsakanin ƙwaƙwalwa da sauran sassan jiki.

Haɗuran ababen hawa, faɗowar gini, faɗowa daga sama, raunukan yaƙe-yaƙe, raunuka daga ayyukan ta'addanci, karyewa/fashewar ƙashin baya, fashewar faifan tsakanin ƙashin gadon baya, tarin fuka(tarin TB) na daga cikin sabuban da ke kawo lahani ga laka.

Tsananin lahani ga laka na iya kasancewa:

1. Tsinkewar laka: wato katsewar laka gaba ɗaya a wuya ko a ƙirji ko kuma a baya.

2. Rauni/lahanin laka: laka na iya samun rauni kawai idan aka yi sa'a lakar ba ta tsinke ba.

Bugu da ƙari, idan laka ta tsinke ko ta samu rauni a wuya, to za a samu katsewar saƙo daga wuya zuwa ƙasa. Matsalar laka a wuya ya fi muni, saboda matsalar na shafar hannaye, ƙafafu da sauran sassan jiki gaba ɗaya.

Haka nan, idan tsinkewa ko raunin a ƙirji ne ko a baya matsalar za ta shafi ƙafafu ne da sauran sassan da ke ƙasa da tsinkewa ko raunin.

Matsalolin da ke biyo bayan tsinkewa ko raunin laka sun haÉ—a da:

1. Kassarewar aikin/motsin gaɓɓai ko sassan jiki.

2. Ɗaukewar jin sanyi, zafi ko taɓawa a fata.

3. Kasa riƙe fitsari da bahaya.

4. Matsanancin ciwo da jin yanayi kamar na tsikara, tafiyar kiyashi, dindiris ko shokin.

5. Wahalar numfashi.

6. Matsalar saduwa da iyali da sauransu.

Likitan tiyatar laka na yin tiyata don haɗe ko buɗe wa lakar hanyarta. Bayan tiyata kuma, likitan fisiyo zai yi duk mai yiwuwa don magance ciwo da nakasar gaɓɓan jiki ta hanyar farfaɗo da aikin lakar.

Source: Physio Hausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN