Wani hari da yan boko haram suka kai a garin Damboa na jihar Borno ya yi sanadin mutuwar wata mata mai juna biyu tare da wasu mutane biyar.
Jaridar Punch ta labarta cewa harin na BH ya yi sanadin raunata wasu mutum bakwai ranar Lahadi. Punch ta ce jami'an sojin Najeriya sun halaka da dama daga cikin yan BH.
Rahotun ya ce yan BH sun yi wa garin Damboa diran mikiya cikin motoci masu bindigogin surke, da babura 12, kuma suka nufi sansanin soji kai tsaye.
Bayanai sun ce yan BH sun sake hadewa suka yi gungu suka koma sansanin sojin ranar Talata 27 ga watan Oktoba, amma soji suka fatattake su. Bayanai daga CJTF a Damboa ya ce yan BH 22 ne soji suka kashe, yayin da soji biyar suka mutu.
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari