An tsare mai jego a Asibiti har tsawon wata 7 bayan haihuwa don rashin kammala biyan kudi

Wani Asibiti mai zaman kansa ya tsare wata mata mai jego da ta haihu a Asibitin na tsawon wata 7 bayan ta kasa biyan kudin da Asibitin ya cajeta.

Rahotanni sun ce matar mai suna Blessing, ta haifi Jariri ne bayan an yi mata tiyata a Asibitin Mojo Hospitals da ke Egbeda Shasha a birnin Lagos. Kuma Asibitin ta caji Blessing Naira  dubu dari uku da hamsin N350,000, amma daga bisani Daraktar ayyukan jinya na Asibitin ya rage mata kudin zuwa Naira dubu dari biyu da hamsin, N250,000.

Blessing ta biya Naira dubu dari da sittin, amma ta kasa biyan sauran cikon kudi Naira dubu casa'in N160,000. Sakamakon haka, Asibitin ta ki ta sallami Blessing har tsawon wata bakwai bayan ta haihu.

Sai dai majiyarmu ta ce mijin Blessing Makanike ne, kuma baya da hanzarin biyan wannan kudi, sakamkon haka suke kira ga jama'a su taimaka masu da cikon kudin N90,000 domin a sallami matarsa daga Asibitin.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN