Dan haya ya kashe mai gidan haya domin ya hana shi shigowa da yanmata barkatai a gidan - Hotuna


Yansandan jihar Anambra sun kama wani matashi mai shekara 21 mai suna Onyeamachi Mmaju bisa zargin kashe mai gidan haya da yake ciki mai suna Nonso Oyikoba, dan shekara 35 a garin Ogidi Ani-Etiti da ke karamar hukumar Idemili na Arewa ranar Talata 6 ga watan Oktoba.

Rahotanni sun ce mai gidan hayan Nonso, ya kalubalanci mai haya a gidansa Onyeamachi cewa yana yawan shigowa da mata barkatai a gidan, ya kuma bukaci ya daina. Amma daga bisani sai rigima ya kaure, har mai haya Onyeamachi ya dauko wuka ya daba wa mai gidan haya a bayansa a wurare da dama.


 

Daga bisani mai gidan haya ya mutu kamar yadda Kakakin hukumar yansanda na jihar Haruna Muhammed ya tabbatar. Yanzu haka dan haya yana fuskantar bincike a sashen SCIID a Shelkwatar yansandan jihar Anambra.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

0/Post a Comment/Comments

Rubuta ra ayin ka

Previous Post Next Post