• Labaran yau


  Yaro mai shekara 7 ya mutu a cikin rijiya a wata jihar Arewa


  Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce  wani yaro mai shekara 7 mai suna Umar Ado, ya mutu a cikin wata Rijiya a Unguwa Uku da ke kusa da titin Yarbawa a karamar hukumar Tarauni a jihar Kano.

   

  Sanarwar haka ta fito daga hannun Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saidu Mohammed  ranar Laraba.


  A cewar Muhammed, "Mun sami kiran gaggawa da misalin karfe 6:00 .na yamma. Nan take muka aika jami'an mu domin ceto yaron da misalin karfe 6:07 na yamma.

  Jami'an mu sun ciro gawar yaron kuma suka kaita Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano inda Likitoci suka tabbatar da mutuwarsa".  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yaro mai shekara 7 ya mutu a cikin rijiya a wata jihar Arewa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama