Yanzu yanzu: Wani magidanci ya makale yayin da yake zina da matar aure (Bidiyo)

Wani bidiyo da ke yawo a yanar gizo ya nuno yadda wata matar aure da ba’a bayyana sunanta ba ta manne da wani abokin shashancinta yayinda suke tsaka da tarawa da junansu. Wasu da abun ya faru a idonsu sun alakanta lamarin da tsafin “Magun” sannan an tattaro cewa lamarin ya afku ne a jihar Ogun, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.


Magun wanda a yaren Yarbanci yake nufin “kada ka hau”, ya kasance asiri mai hatsari sosai wanda magidanta kan yi amfani da shi wajen hukunta mazan banza masu neman matansu. A wani labari na daban, ‘Yan sandan kasar Italiya sun damke wasu ma’aurata da suke saduwa a cikin mota tare da yin karantsaye ga dokar kebancewa ta coronavirus.


Ma’auratan da aka gano mijin dan asalin kasar Egypt ne mai shekaru 23 sai kuma matar ‘yar asalin kasar Tunisia ce mai shekaru 40. An kama su ne a kan titin Mecenate da ke birnin Milan, inda cutar coronavirus ta fi barkewa. Kamar yadda jaridar Daily Mail UK ta wallafa, wnai dan sanda ne da ke bakin aiki ya kama ma’auratan.

Karin rahoto a kan hakan ya bayyana cewa dokar kebancewa da aka saka ta coronavirus ta haramtawa mutane biyu zama a waje daya a cikin mota. Amma kuma ko a yayin sanar da dokar, ba a tabbatar da cewa za a hukunta ma’aurata ba a kan hakan. Kasar Italiya ta bayyana a cikin daya daga cikin kasashen da mugunyar cutar coronavirus ta addaba a duniya. Hakan kuwa yasa aka rufe kasar don gudun yaduwarta.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt


Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN