Kasar UAE ta yaudari duniyar Musulunci yayinda ta hada kai da Isra'ila

Hadaddiyar daular Larabawa UAE ta yaudari duniyar Muslunci da Falasdinawa ta hanyar shiga sulhu da Isra'ila, Shugaban koli na kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya bayyana a jawabi. Falasdinawa sun nuna rashin amincewarsu da hakan saboda zai raunata yarjejeniya da kasashen Larabawa sukayi na yanke alaka da Isra'ila kafin tabbatar da kasar Falasdin.

Falasdinawa sun gudanar da zanga-zanga suna kona tutocin UAE domin nuna fushi, cewar AlJazeera. "Tabbas, yaudarar UAE ba zai wanye ba, amma ba za'a manta da hakan ba. Sun bari Yahudawa su shiga yankin kuma suka mana da Falasdin," Khamenei ya bayyana ranar Talata. "Wannan abin kunyan zai cigaba da bin kasar UAE... Ina fatan zasu farka daga baccinsu kuma su gyara abinda sukayi." Wani jami'in gwamnatin UAE ya yi watsi da jawabin Khamenei.

"Hanyar samar da zaman lafiya da cigaba ba zai yiwu ba ta hanyar zage-zage da kalaman batanci ba," Jami'in ma'aikayar harkokin wajen UAE,"amal Al-Musharakh. "Ire-iren wadannan kalaman na da barazana ga zaman lafiya a yankin." Kasar Isra'ila da UAE na sa ran amfana da juna ta fannin tattalin arziki, a wata alakar ta farko irinta tsakanin wata kasar Larabawa da Isara'ila cikin shekaru sama da 20.

Falasdinawa sun bayyana mamaki da bacin ransu kan yadda wannan mataki zai raunata doguwar alaka da kirar da Larabawa ke yiwa Isra'ila su janye daga yankunan Falasdinawa kuma amince da Falasdin a matsayin kasa. Manyan jami'an kasar UAE sun yi kokarin basar da Falasdinawa ta hanyar cewa sun shiga sulhu da Isara'ila ne saboda ta dakatad da shirin sake kwace filaye a yankin Kudus, kuma Firam Ministan Benjamin Netanyahu ya amince da hakan.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN