Yanzu yanzu: Hukumar Kwastan ta gano sansanin boko haram guda 5 a Abuja da kewaye

An gano sansanin yan boko haram guda biyar a cikin gandun dajin Abuja, jihohin Nassarawa, da kuma Kogi, kuma suna shirin kai hari ga zababbun wurare kamar yadda hulkumar Kwastam ta fitar.

Jaridar Daily Trust ta labarta cewa hukumar Kwastam NCS, ta ankarar da jami'anta a wata takarda na cikin gida, daga ranar 20 ga watan Agusta zuwa ranar 4 ga watan Satumba, wanda wani Kwantorola ya sa ma hannu a Shelkwatar hukumar da ke Abuja.

Wani bayani da ya fito daga shugaban NCS na kasa Kanar Hameed Ali mai murabus, ya ce "  Akwai wanzuwar sansanin yan ta'adda na boko haram" a ciki da wajen yankin birnin tarayya".

"Akwai rahotannin cewa suna shirin kai hare hare a kan zababbun wurare a Abuja, kuma sun kafa sansaninsu a zababbun wurare".

Takardar da ta fito daga babban Kwantorola na Kwastan na kasa, ta zayyana wurare biyar da ta ce akwai wanzuwar sansanin yan boko haram, wanda suka hada da:

1. Gandun dajin Kunyam, a kan hanyar babban filin jirgin sama na Abuja, kusa da gidajen ma'aikatan hukumar DIA
2. Gandun daji na Rubochi zuwa Gwagwalada a babban birnin tarayya
3. Gandun daji na Kwaku, a yankin Kuje na babban birnin tarayya
4. Gandun dajin Unaisha a karamar hukumar Toto a jihar Nassarawa
5. Gandun dajin Gegu, kusa da garin Idu a jihar Kogi

Haka zalika takardar ta umarci sashen leken asiri na NCS su gaggauta fara aiki, yayin da aka sanar da yan sanda domin daukan matakin da ya dace.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN