‘Buri Na Na Zama Babbar jaruma A Masana’antar Kannywood -Amina Uba Hassan

Da farko zamu so ki gabatar mana da masu karatu sunan ki da dan takaitaccen tarihin ki?

Suna na Amina Uba Hassan an haife ni a garin kaduna, a nan nayi Primary School dina da Secondary School dina, sannan nayi Diploma na duk a cikin garin Kaduna.

A wace shekara kika shiga masana’antar Kannywood?

Eh a wannan shekarar na shiga masana’antar Kannywood.

Shekarar da muke ciki kenan na 2020?

Eh a wannan shekarar ta 2020 na shiga.

Mai ya ja ra’ayin ki ki ka shiga wannan masana’anta ta Kannywood?

Eh to ni mutum ne mai san rawa da waka, ban taba kai hankali na zuwa ga acting ba, nafi son waka da rawa saboda shine nake da ra’ayi, amma wani abu ne ya faru zuwa na Abuja, wasu ‘yan Nollywood suna shooting to akwai abokin mu dake cikin masu shirya fim din, to sai babban jarumin fim din ashe yana ta kallo na yana ganin abin da nake yi, sai ya ke tamabaya na meyasa bazan yi acting ba, sai na ce masa mai yasa yace haka?

Sai yace kawai yaga yanayin acting a waje na ne yana ta kallo na dadai sauransu, bayan nan da na koma gida muka zauna da kawaye na muna ta hira kawai sai naji bari nima na gwada na gani tinda bama shi kadai ba mutane da yawa sun yimin magana tun kafin lokacin, sai n ace to bara na gwada na gani.

Daga zuwa lokacin da kika ji cewa zaki fara zuwa yanzu, akwai fina-finan da kika fito a ciki?

Aa ban fara ba, an dai gabatar da ni a matsayin jarumar da zata fita a cigaban wani fim mai suna ‘Jaruma’ to akwai na biyun shi wanda nine zan fita a matsayin jaruma ciki, saidai kuma akwai producers wanda suke so su bani wasu fina-finan to amma dai tukunna yanzu ‘Jaruma2’ shine wanda aka gabatar dani mutane suka san ni zan fita a cikin shi, to bayan wannan ne nake tunanin zan ci gaba da fita wadansu amma yanzu ban riga na fara ba.

Kasancewar ki sabuwar jaruma a masana’antar, gashi kina shirin taka rawa da fitacciyar jaruma wato Maryam Yahaya a fim din ‘Jaruma2’, ya kike ganin kasantuwar hakan a ranki?


Ammm… ba abinda nake ji saboda nasan abu ne wand azan iya yi kuma rol din da aka bani rol ne wanda nasan zan iya yinshi sosai saboda kasan kowa da irin baiwar da Allah yayi masa, misali tun kafin na fara tun ma kafin a fara nuna ni ko ina ya dauka Amina zata fara fim… Amina zata fara Fim… to wannan kadai yana nuna min cewa zan iya, bana jin komai a shirye nake.

To idan muka dawo batun iyali fa, shin kina da aure ne ko kin taba yi?

eh na taba aure harda da

wadansu kalubale kika fuskanta daga gida kasancewar zaki fara fim musamman a bangaren iyaye?

Gaskiya ban fuskanci wani kalubale ba, kuma bana fuskantar wani kalubale kuma iyaye na wato mahaifiyata da mahaifi na duka basu da rai sai kanni na wanda duk suna gidajen mazajen su, ni ce babba kuma bana fuskantar wani kalubale gaskiya indai ta wannan fannin ne babu.

To kasancewar kowa na da buri, ke a naki wane mataki kike da burin kikai a nan gaba?

Duk abin da kake a rayuwa ko wajen aiki, masana’anta kasuwa dama wasu wuraren, zaka so a ce yau kaine aka fi zuwa siyan abu a wajen ka, saboda haka ni kuma abinda zan iya cewa shine a nan gaba inada burin na zama babbar jaruma wanda duniya baki daya zasu sanni su kuma dinga jin labari  na.

To bangaren karatu kuma fa, kina wani mataki ne?

A bangaren karatu na tsaya a Diploma na ban cigaba ba amma ina tunanin cigaba saboda kamar ina makaranta ne ina aiki amma kamar sana’a ta ne ta rinjaye karatu na, amma dai n agama Diploma na ne a Mechanical Engineering a nan KADPOLY SCT amma ina tinanin karasa wa kila cikin shekara mai zuwa insha Allah.

Wane ne tauraron ki a masana’antar Kannywood?

Adam A. Zango

Tauraruwa fa?

Jamila na gudu

A kan yi miki lakabi da ‘Amina Rani’ a ina ya samo asali?

Kamar yanda na fada maka ina san rawa da waka, akwai wani fita da muke ko wace sallah kamar babbar sallah mukan yi indian show a hall haka inda muke gayyatan mutane, muyi gasar rawa haka na wakokin india mi rawa, ni kuma babbar jaruma ta wanda nake matukar so a india itace Rani, saboda haka sai wandanda muke tare da su muke rawa tare suka fara kira na da ‘Amina Rani’, kaji inda aka samo Amina Rani.

To idan muka dawo bangaren abinci fa, wanne kika fi so?

A gaskiya bangaren abinci wanda nafi so shine shinkafa da mai da yaji.

Tambaya ta karshe, wane sako zaki iya aikawa zuwa ga masoyan ki?

To na farko dai ina godiya da son da suka nuna min tun kafin na fara, sai kuma na ce Allah saka musu da alkhairi kuma insha Allahu bazan basu kunya ba.

To mun gode  sosai da ki ka bamu hadin kai dari bisa dari sannan muna fatan koda nan gaba muka bukaci hakan daga gareki zamu samu.

Insha Allahu, nima nagode.

Source: Leadership a yau (Leadership hausa)Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN