Za mu taimaka wa wadanda ambaliyar ruwa ya shafa a jihar Kebbi>>Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin kawo dauki da taimako ga wadanda ambaliyar ruwa ya shafa a jihar Kebbi.

A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Buhari ya ce " Jihar Kebbi ta zama zakaran gwajin dafi wajen shirinmu na noman shinkafa a cikin gida domin farfadowa da aikin gona. Na tausaya wa iyalai da wannan ambaliya ya shafa . Za mu yi aiki tare da Gwamnatin jihar Kebbi domin ganin mun taimaka wa wadanda lamarin ya shafa" inji shugaba Buhari.

Haka zalika, tun farko Buhari ya nuna bakin cikinsa kan ambaliyar ruwa da ta shafi jihar Kebbi, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da bata dubban Hekta na gonaki. Wanda ya ce babban koma baya ne wajen kokarin Gwamnatin tarayya na ganin an noma shinkafa a cikin gida domin kawo karshen tsarin shigowa da shinkafa daga kasashen waje.

Ya ce labarin aukuwan wannan ambaliya bai kamata ya zo a daidai lokacin da manoma da yan Najeriya ke dakon ganin an girbe amfanin gona mai yawa ba, domin rage yadda ake fama da hauhawan farashin kayan abinci a kasuwanni.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt


Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN