• Labaran yau


  Yanzu yanzu: Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya dakatar da hukumar Hisbah na jihar

   


  Gwamnan  jihar Sokoto  Aminu Tambuwal, ya dakatar da hukumar Hisbah na jihar bisa zargin "Rarrabuwa"

  Daily Trust ta labarta cewa ba wannan ne karo na farko da aka dakatar da hukumar ba,. Idan ba ku manata ba, Kwamishinan harkokin addini na jihar Sokoto, Mani Maishinku Katami, ya sanar da dakatar da hukumar Hisbah na jihar Sokoto shekara uku da suka gabata, kafin daga bisani aka dage dakatarwar.


  A wata sanarwa da ta fito daga Hadimin Gwamna kan harkar watsa labarai Muhammad Bello, ya ce an kafa Kwamitin mutum 36 domin daidaita  ayyukan hukumar tare da samar da shawara kan ka'idan yadda Hisbah ya kamata ta gudanar da ayyukanta bisa tsarin doka da ta kafa ta.


  An nada Wazirin Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu a matsayin shugaban Kwamitin, yayin da Sakataren din-din-dim a ofishin Kabinet  Alhaji Bande Rikina ya zama Sakataren kwamitin.  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yanzu yanzu: Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya dakatar da hukumar Hisbah na jihar Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama