Minista Malami ya rage wa masu ambaliyar ruwa radadi da N11m a Masarautar Gwandu


 

Ministan shara'a kuma Attoni Janar na Najeriya Abubakar Malami, ya sanar da bayar da taimakon zunzurutun kudi har Naira Miliyan goma sha daya N11m ga wadanda ambaliyar ruwa ya rutsa da su a Masarautar Gwandu da ke Jihar Kebbi.

 

PM News ta labarta cewa Malami ya ce za a bayar da kudin ne ta kungiyoyinsa na taimakon jama'a guda biyu, Khadimiyya For Justice and Development da kuma Khadi Malami Foundation.

 

Ministan ya sanar da bayar da wannan taimako ne yayin ziyara da ya kai wa Mai Martaba Sarkin Gwandu  Alhaji Muhammadu Ilyasu-Bashar a Fadarsa da ke Birnin Kebbi.

 

Ya ce wadanda ambaliyar ruwa ya rutsa da su a garin Birnin kebbi, za a raba masu Naira Miliyan biyu N2m, yayin da sauran kananan hukumomi guda tara da ambaliyar ruwan ya shafa za a raba masu Naira Miliyan daya kowane karamar hukuma domin taimaka wa wadanda ambaliyar ya shafa.

 


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari