Bidiyon lalata da Amarya a Sokoto : Gwamna Tambuwal ya bayar da umurnin yin bincike

 


Gwamna Aminu Tambuwal ya bayar da ummarnin binciken wani matashi da ya nada bidiyon yadda ya yi lalata dawata yarinya kuma ya wallafa bidiyon wasu shekaru bayan aukuwan lamarin domin ya bata auren yarinyar a jihar Sokoto.

Hadimin Gwamna Tambuwal kan harkar watsa labarai Muhammad Bello ya ce, ba wai Gwamna Tambuwal ya ce a kama kowa bane, sai dai ya ce wa Kwamishinan yansanda ya yi adalci wajen binciken lamarin kuma a tabbatar cewa an hukunta wanda baya da gaskiya.

Ya ce hatta mahaifiyar yarinyar Safiya Umar ta tabbatar da umarnin Gwamna kan lamarin.


Wanda ake zargi da aikata laifin mai sun Baffa Hayatu Tafida, da ne ga wani mai ba Gwamna Tambuwal shawara, kuma yana da shekara 17 a Duniya lokacin da lamarin ya faru a 2017.


Yarinyar tana da shekara 16 lokacin da Baffa ya lallabeta ya kaita dakin wani Otal da ya kama inda ya aikata wannan lalata da ita kuma ya nada a wayarsa ta salula.


Mahaifiyar yarinyar Safiya Umar ta bayya cewa wanda ake  zargin ya aika ma wadanda suke nemanta aure da sakon bidiyon domin ya lalata aurenta.

Ta kara da cewa " Irin wadannan shugabanni ne (Aminu Tambuwal) al'umma ke bukata wadanda ke tashi tsaye domin ganin an yi wa talakawansu adalci" 

Sai dai tsohon Kwamandan Hisbah na jihar Sokoto Dr Adamu Bello Kasarawa, ya ce yanzu maganar na hannun yansandan jihar Sokoto bisa umarnin Gwamnan jihar.Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN