Yanzu yanzu: Buhari ya taya Obaseki murnar sake lashe zaben Edo


Shugaban kasa Muhamadu Buhari ya taya Godwin Obaseki da jam'iyyar PDP murnar sake lashe zaben gwamnan jihar Edo, da aka gudanar ranar Asabar 20 ga watan Satumba, 2020. Shugaba Buhari a cikin wata sanarwa daga mai tallafa masa ta fuskar kafofin sada zumunta, Bashir Ahmad, ya bukaci Obaseki da ya nuna dattako akan wannan nasara.


A ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba, Hukumar zabe INEC ta sanar da Godwin Obaseki a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan samun kuri'u 307,955.Shugaban kasa Buhari ya ce, "Kokarina na ganin an gudanar da sahihin zabe ya tabbata, saboda ba don anyi sahihin zabe ba, da bangon siyasa da demokaradiyyar kasarmu ya ruguje."Wannan shine karo na biyu da Obaseki ke yin nasara a kan Ize-Iyamu, inda a shekarar 2016 ma hakan ta kasance sai dai a lokacin Obaseki ya yi takara a karkashin APC yayin da Ize-Iyamu ke PDP.


INEC ta sanar da cewa Obaseki ya zama zakara ne a zaben gwamnan bayan samun kuri'u mafi rinjaye na 307,955 inda mai biye masa Ize-Iyamu ya samu kuri'u 223,619. Wanda ya zo na uku a zaben shine dan takarar jam'iyyar SDP da kuri'u 323, sai na hudu dan takatar jam'iyyar LP da ya samu kuri'u 267.


Hukumar zaben ta ce adadin masu zabe da aka tantance domin kada kuri'a a jihar 557,443, yayin da adadin kuri'u masu sahihanci 537,407. Jimillar kuri'un da masu zabe suka kada 550,242, sannan kuri'un da suka lalace kuma 12,835. Jam'iyyu 14 ne suka gabatar da 'yan takara a zaben da aka yi a ranar Asabar 19 ga watan Satumban 2020.

Source: LegitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN