• Labaran yau


  El-Rufai ya tabbatar da mutuwar Sarkin Zazzau, ya sanar da lokacin jana'iza


  Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya tabbatar da rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, bayan gajeriyar rashin lafiya.

  Sarkin ya rasu a asibitin sojoji na 44 da ke Kaduna a ranar Lahadi.

  "Cike da alhini nake tabbatar da mutuwar baban jiharmu, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dr, Shehu Idris Idris," El-Rufai ya wallafa a Facebook.

  Ya kara da cewa, "Ya rasu a asibtin sojoji na 44 da ke Kaduna a yau bayan gajeriyar rashin lafiya. Za a yi jana'izarsa a garin Zazzau da karfe 5 Insha Allah.


  "Za a kiyaye dukkan dokokin dakile yaduwar annobar korona a yayin jana'izar da karbar makokinsa.

  “Na sanar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan wannan babban rashin kuma yana mika ta'aziyyarsa.

  "Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, zai jagoranci wakilan gwamnatin tarayya zuwa Zaria domin ta'aziyyar mai martaba a masarautar Zazzau da jihar Kaduna.

  “Mun rasa babban abun alfaharinmu, mai cike da hikima sannan uban kowa. Allah ya bashi masauki a Aljanna Firdau. Amin"


  Majiyoyi da dama da suke da kusanci da fadar sarkin sun tabbatar da rasuwarsa a yau Lahadi.

  Marigayi Sarkin Zazzau shine Sarki na 18 na Fulani a masarautar Zazzau. Ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.

  Majiyoyi da dama sun tabbatar wa Legit.ng cewa, basaraken ya rasu a asibitin 44 da ke Kaduna wurin karfe 11 na safiyar Lahadi.

  "Tabbas Allah ya yi wa Sarki rasuwa. Ya kwanta rashin lafiya tun a ranar Juma'a kuma an kai shi asibiti inda ya rasu.

  "Nan babu dadewa za a dawo da gawarsa Zaria domin fara shirin jana'izarsa," wata majiya mai kusanci da Iyan Zazzau ta tabbatar.

  Source: Legit  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: El-Rufai ya tabbatar da mutuwar Sarkin Zazzau, ya sanar da lokacin jana'iza Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama