Hotunan yadda dandazon jama'a suka cika wajen jana'izar Sarkin Zazzau

Da yammacin yau Lahadi, 20 ga watan Satumba ne gawar Marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ta isa Zaria, inda za a gudanar da jana'izarsa da misalin karfe biyar na yamma.


An gano dandazon jama’a da suka taru domin jana’izar marigayin Sarkin ya rasu ne a yau Lahadi, a asibitin sojoji na 44 da ke birnin Kaduna, sashin Hausa na BBC ta ruwaito. Sarkin ya rasu yana da shekaru 84, ya kuma shafe shekaru 45 kan karagar mulki.Da farko mun kawo maku cewa Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya tabbatar da rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, bayan gajeriyar rashin lafiya. Sarkin ya rasu a asibitin sojoji na 44 da ke Kaduna a ranar Lahadi.


"Cike da alhini nake tabbatar da mutuwar baban jiharmu, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dr, Shehu Idris Idris," El-Rufai ya wallafa a Facebook. Ya kara da cewa, "Ya rasu a asibtin sojoji na 44 da ke Kaduna a yau bayan gajeriyar rashin lafiya. Za a yi jana'izarsa a garin Zazzau da karfe 5 Insha Allah. 
"Za a kiyaye dukkan dokokin dakile yaduwar annobar korona a yayin jana'izar da karbar makokinsa. “Na sanar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan wannan babban rashin kuma yana mika ta'aziyyarsa.


"Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, zai jagoranci wakilan gwamnatin tarayya zuwa Zaria domin ta'aziyyar mai martaba a masarautar Zazzau da jihar Kaduna. “Mun rasa babban abun alfaharinmu, mai cike da hikima sannan uban kowa. Allah ya bashi masauki a Aljanna Firdau. Amin" 


Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN