Wani me aski, Atighan Sam ya zargi jami'in dansanda da shiga gidansa ya lalata masa kayan amfani da kuma sace masa kudi 280,000. Lamarin ya farune a Diobu dake birnin Fatkwal ta jihar Rivers da misalin karfe 12 na daren Juma'ar data gabata.
Sam yace yaji dansandan na tambayar makwabta cewa a nuna masa gidansa dan hakane ya samu ya tsere kamin ya sameshi a ciki.
Yace dansandan ya shigar masa gidane bisa rakiyar wasu abokan aikinsa 2 inda yayi zargin ya kai masa harinne saboda yaki biya masa kudin giyar da ya sha shi da wasu abokansa a wata mashaya.
Me Askin ya bayyana cewa ya kaiwa 'yansanda korafi kan lamarin inda kuma an gayyaci dansandan da ake zargi me suna Usman dan yin bincike.
hutudole
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/
Tags:
LABARI