Yanzu-yanzu: Jami'an tsaro sun samu nasarar bindiga kasurgumin dan bindiga Bobisky


Wani kasurgumin dan fashi kuma mai garkuwa da mutane da ya addabi jihar Rivers, Honest Digbara wanda aka fi sani da Bobisky, ya gamu da ajalinsa hannun jami'an hukumar yan sanda. An bindige dan bindigan wanda aka dade ana nema ruwa a jallo ne ranar Asabar. Al'ummar jihar sun shiga murna da farin ciki yayinda suka samu labarin mutuwan Bobisky.


Gabanin samun nasarar hallakashi, gwamnati ta yi alkawarin kudi milyan 30 ga duk wanda ya ke da labarin inda dan bindiga yake. An damke shine a wani harin bazata da hukumar yan sandan Rivers ta kai garin Korokoro dake karamar hukumar Tai ta jihar. Kisan Bobisky ya biyo bayan hallaka dan bindigan da aka dade ana nema ruwa a jallo, Terwase Agwaza Gana,da jami'an Sojin 'Special forces' a jihar Benue sukayi.


Yace, "Misalin karfe 12:00 na ranar Talata, mun samu labarin shahrarren dan bindiga Terwase Akwaza Agbadu wanda aka fi sani da Gana na hanyar Gbese-Gboko-Makurdi. "Dakarun rundunar Operation ‘Ayem Akpatuma III’ suka bazama tare hanyar." "Misalin karfe 13:00, an yi musayar wuta tsakanin Soji da Gana inda aka kasheshi." Kwamandan ya ce an damke yaran aikinsa 40 da manyan makamai.

Source; LegitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN