• Labaran yau


  Daga yanzu zuwa watan Disamba kayan masarufi zasu ci gaba da yin tsada - CBN


  Babban bankin Najeriya,CBN ya bayyana cewa nan zuwa watan Disamba hauhawar farashin kayan masarufi zai karu zuwa kaso 14.15 cikin 100.  

   

  A watan Yuli da ya gabata hauhawar kayan Masarufin ya tsaya ne a kaso 12.82. CBN a wani Rahoto da ya fitar jiya, Juma'a yace amma akwai shirye-shiryen da yake na saukakawa mutane tsadar farashin kayayyakin. 

   

  Rahoton ya kara da cewa za'a samu tsadar farashin kayanne saboda matsalar kudi da gwamnati ke fama da ita sannan kuma za'a samu matsala wajan daukar aiki saboda rashin karfin sayayya da 'yan kasa ke dashi.   

   

  Ya kuma bayyana cewa wannan matsala cutar Coronavirus/COVID-19 ce ta zo dashi wanda ya taba kasashen Duniya baki daya. 

  hutudole


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Daga yanzu zuwa watan Disamba kayan masarufi zasu ci gaba da yin tsada - CBN Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama