Rahotanni daga jihar Imo sun bayyana cewa, ‘yan ta’adda a Egbu dake Owerri da Owerre Nkworji dake karamar hukumar Nkwerre sun kaiwa ‘yansanda hari inda suka kwace musu bindigu da kuma daddatsa daya daga ciki wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarsa.
Ranar Litinin ne ‘yan Bindigar suka kaiwa ‘yansandan dake Nkwerre hari inda suka daddatsa daya daga ciki sannan suka kona motar aikin ta ‘yansandan.
An garzaya da wanda aka sara Asibiti ranar Talata saidai daga baya ya rasu, kamar yanda Rahoton Punch ya tabbatar.
Hakanan kuma wasu ‘yan Bindigar sun kai wa ‘yansanda hari a Egbu inda suma suka kwace musu bindigu da sarar wani dansanda amma daga baya an garzaya dashi Asibiti.
Kwamishinan ‘yansandan Jihar, Isaac Akinmoyede da aka tuntubeshi ya tabbatar da cewa, an kwacewa ‘yansandan Bindigu amma babu wanda aka kashe
Hutudole
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/